Firayiminstan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira ga jami'an gwamnatin kasar, su tabbatar da tsare gaskiya tare da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
Li Keqiang wanda ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wajen taron majalisar gudanarwar kasar, ya kuma bukaci a kara zage damtse wajen yaki da cin hanci.
Taron ya kuma samu halartar mataimakan firayiministan da suka hada da Zhang Gaoli da Wang Yang da Ma Kai da kuma sakataren hukumar ladaftarwa ta tsakiya ta jam'iyyar kwaminis ta Sin, Wang Qishan.
Da yake yabawa nasarorin da aka samu wajen tsare gaskiya, da yaki da cin hanci a harkokin shugabanci, Li ya ce, har yanzu akwai matsalolin da suke bukatar managartan matakan magance su, yana mai bukatar a kara kokari wajen zabar jagorori da inganta ayyukan gwamnati da kuma amfani da kafar intanet wajen inganta ayyukan gwamnati.
Ya kara da cewa, ya kamata gwamnatocin a dukkan matakai su ci gaba da rage kudin haraji da kashe-kashen kudi, inda ya ce, kamata ya yi a rika binciken almundahana tare da hukunta masu laifi.
Firayiminstan ya kuma yi kira da a kara sanya idanun kan abubuwan da suka shafi kadarorin da kamfanoni gwamnati da bangaren harkokin kudi da kuma muhimman ayyukan samun riba da kasar ke yi a ketare. (Fa'iza Mustapha)