Li ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki a lardin Yunnan dake shiyyar kudu maso yammacin kasar Sin, tsakanin ranakun Litinin zuwa Laraba, wato gabanin kamawar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin.
A lokacin da ya ziyarci wani kauye dake da matalauta a wannan lardi, firaministan na Sin, yayi alkawarin tallafawa iyalai masu fama da halin kuncin rayuwa.
Ya kara da cewa, gwamnatin Sin zata yi kokari wajen gyaran gidaje a yankunan karkara.
Shirin yaki da talauci na kasar Sin tsakanin shekarar 2016-2020, ya nanata aniyar gwamnati na fitar da dukkan al'ummar kasar daga kangin talauci nan da shekarar 2020. Daga karshen shekarar 2015, kasar Sin nada matalauta da yawansu ya kai miliyan 55.75.
A lokacin da firaministan ya ziyarci wasu kananan kasuwanni, ya bukaci yan kasuwar dasu kara kiyaye ingancin kayayyakin abinci, kana su samar da yanayin kasuwanci mai inganci.