A cikin sakon, Li Keqiang ya kadu a samu labarin harin ta'addanci da aka kai birnin Berlin a daren ranar 19 ga wata, harin da ya haddasa mutuwa tare da raunata mutane da dama. A madadin gwamnatin kasar Sin, Li Keqiang ya mika ta'aziyya ga iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon harin, sannan ya jajantawa iyalan wadanda suka jikkata, tare da fatan samun sauki ga mutanen da suka ji rauni. Sin tana goyon bayan kasar Jamus a kokarin da take yi na yaki da ta'addanci da tabbatar da tsaron kasa, kana yana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Jamus da sauran kasashen duniya a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya. (Zainab)