Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da masana da 'yan kasuwa domin jin ra'ayoyinsu game da rahoton aikin gwamnatin da aka saba fitarwa a ko wace shekara.
Wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ta bayyana cewa, a yayin ganawar ta ranar Jumma'a, masana da 'yan kasuwar sun yi musayar ra'ayoyi tare da ba da shawarwari game da ayyukan gwamnatin kasar ta Sin.
A nasa bangare, firaminista Li ya yi wa mahalarta taron bayani game da tarin nasarorin da gwamnatin Sin ta cimma a shekarar da ta gabata a bangarorin da suka hada da kara samar da guraben ayyukan yi, matakan bunkasa tattalin arziki, da kuma inganta rayuwar al'ummar Sinawa.
Firaminista Li ya kara da cewa, a wannan shekara tattalin arzikin kasar Sin zai fuskanci matsin lamba matuka, sakamakon rashin tabbas da sarkakiya game da tsarin harkokin siyasar duniya, gami da kalubalen da manufofin tattalin arziki suke fuskanta.
Amma duk da haka, ya ce, babu abin da zai shafi tattalin arzikin kasar ta Sin ba. Yayin da a nata bangaren, gwamnatin za ta ci gaba da daukar matakan inganta shi, ta yadda zai ci gaba da bunkasa yadda ya kamata.
Firaminista Li ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da neman hanyar ci gaba cikin lumana, da aiwatar da shawarwarin raya kasa guda biyar, wato kirkie-kirkire, tsare-tsare, raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, bude kofa ga kasashen waje da yin musaya, da bunkasa matakan samar da kayayyakin yayin da kuma ake yin gyare-gyare.(Ibrahim)