Li Keqiang ya bayyana cewa, cikin shekara daya da ta gabata, yayin da ake fuskantar matsalar raguwar tattalin arzikin a duniya, tattalin arzikin Sin ya bunkasa, inda yawansa ya karu da kashi 6.7 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar baya.
Wannan al'amari, ya sanya tattalin arzikin Sin kasancewa kan gaba cikin jerin kasashe masu karfin tattalin arzikin a duniya, sannan, yawan gudummawar da Sin ta bayar wajen karuwar tattalin arzikin duniya ya zarce kashi 30 cikin dari.
Ya ce an kyautata tsarin tattalin arzikin ne ta hanyar samar da sabbin ayyukan yi ga mutane fiye da miliyan 13 a shekaru hudu a jere, inda ya ce kwararrun na kasashen waje sun bada gudummawa wajen cimma wannan sakamako.
Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin ta bada goyon baya ga yin ciniki da zuba jari cikin 'yanci, kuma za ta ci gaba da mara baya ga kamfanonin da suka shiga kasuwa, da janyo hankalin masu zuba jari na kasashen waje, tare da kara koyo fasahohin zamani.
Har ila yau, ya ce Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci, tare da saukaka dokokinta, ta yadda za ta jawo hankalin masu zuba jari da kamfanonin kasashen waje. (Zainab)