in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta hana fasinjoji daga filayen jirgin sama guda 10 su je Amurka tare da na'urorin da girmansu ya fi na wayar salula
2017-03-22 12:28:33 cri

Jiya Talata ne ma'aikatar tsaron cikin gida ta kasar Amurka ta sanar da cewa, sakamakon dalilan tsaro, ya sa nan take ta yanke shawarar hana fasinjoji daga filayen jiragen sama 10 na kasashen duniya 8 da suka hada da Jordan, Turkey, Saudiyya, Kuwait, Masar, Qatar, hadaddiyar daular Larabawa da Morroco wadanda za su je Amurkar ta jiragen sama kai tsaye tare da na'urorin lantarki da girmansu ya fi na wayar salula.

Sanarwar ba ta yi karin bayani kan dalilin da ya sa Amurka ta zabi wadannan filayen jirgin sama guda 10 daga wadannan kasashe 8 ba, kana ba ta ce uffan ba game da tsawon lokacin da aka yi hakan, da kuma yiwuwar ko za'a kara yawan filayen jiragen saman a nan gaba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China