in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya gabatar da kasasfin kudin gwamnatinsa na farko
2017-03-17 10:43:21 cri
Shugaban Amurka Donalda Trump ya gabatar da kasasfin kudinsa na farko, wanda ya zaftare kudaden hukumomin da ma'aikatun gwamnati domin kara yawan kudin da za a kashe a bangaren tsaro.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Daraktan kula da kasafin kudi na Fadar White House Mick Mulveney, ya ce kudurin Kasafin ya bayyana wa 'yan majalisar dokokin kasar da sauran jama'a bangaren da gwamnatin Trump ta sa a gaba, inda ta bada muhmmaci ga shirin sake ginawa da farfado da tsaron kasar.

Ya ce a cikin wannan kasafin na farko, gwamnatin ta yi kira da rage kudaden da da ake kashewa hukumomi da ma'aikatun gwamnati, al'amarin da zai soke dukkan wasu shirye-shirye da rage yawan ma'aikata a shekarar kudi ta 2018 da za a fara a ranar 1 ga watan Oktoban bana.

Domin karfafa rundunar sojin Amurka da tsaron iyaka, kudurin ya nemi ware dala biliyan 52.3 ko kuma Karin kashi 10 ga ma'aikatar tsaro da kuma dala biliyan 2.8 ko kuma Karin dala kasha 6.8 ga ma'aikatar tsaron cikin gida. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China