in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a dauki matakan dakatar da gwajin nukiliya a Koriya ta Arewa, in ji sakataren harkokin wajen Amurka
2017-03-18 13:57:54 cri
Jiya Jumma'a, sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Koriya ta Kudu ya bayyana a birnin Seoul cewa, ba za a ci gaba da nuna hakuri ga kasar Koriya ta Arewa ko kadan ba, kasar Amurka za ta dauki matakai yadda ya kamata domin matsa lamba ga kasar da ta dakatar da gwajin nukiliyarta.

Mr. Tillerson, ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai da aka yi a birnin Seoul, inda ya kuma halarci taron tare da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Yun Byung-se.

A yayin taron, ya kuma bayyana cewa, za a dauki matakai iri daban daban ta fuskar diflomasiyya, tsaro, tattalin arziki da dai sauransu, domin kawo karshen gwajin nukiliyar kasar Koriya ta Arewan. Ya ce, ya kamata kasar Koriya ta Arewa ta gane cewa, ba za ta tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar tattalin arzikin kasar ba, sai ta dakatar da dukkan gwajin nukiliyar da take yi a kasar domin raya makaman nukiliya.

Ya kuma kara da cewa, ba a son ganin tashin rikice-rikice a tsakanin kasashen da abin ya shafa, amma idan kasar Koriya ta Arewa ta kalubalanci tsaron sojojin kasar Koriya ta Kudu da na sojojin kasar Amurka wadanda suke zaune a Koriya ta Kudu, kasar Amurka za ta mai da martani gare ta.

Manufar yin hakuri da gwamnatin kasar Amurka dake karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ta dauka kan kasar Koriya ta Arewa ta nuna cewa, Amurka ba za ta yi shawarwari da Koriya ta arewa ba, kuma za t ci gaba da aza mata takunkumi kafin Koriya ta Arewa ta nuna sahihanci wajen yin shawarwari da sassan da abin ya shafa.

Manufar da Mr. Tillerson ya bayyana kan zirin Koriya ta janyo hankulan al'ummomin kasar Koriya ta Kudu sosai, babbar jam'iyyar demokuradiya da 'yancin kai ta kasar ta bayyana cewa, kada a dauki matakan da za su haddasa tabarbarewar harkokin soji a yankin zirin Koriyar, ta kuma jaddada cewa, abu mai muhimmanci shi ne, a dawo da sassa daban daban da abin ya shafa teburin yin shawarwari, yayin da matsawa kasar Koriya ta Arewa lamba domin dakatar da gwajin nukiliyarta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China