in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Amurka
2017-03-19 12:54:13 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, dake ziyarar aiki a birnin Beijing tun daga ranar 18 ga wata.

A yayin shawarwarin, Wang Yi ya bayyana cewa, bayan da Donald Trump ya hau kujerar shugaban kasar Amurka, ana raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata bisa kokarin da bangarorin biyu suke yi. Kamata ya yi kasashen biyu su kara yin mu'amala da juna don tabbatar da ganawa a tsakanin shugabannin kasashen biyu cikin nasara. Kana kasashen biyu su kara maida hankali kan hadin gwiwarsu, da yin mu'amala a tsakanin manyan shugabannin biyu, da fadada hadin gwiwa a fannonin diplomasiyya, tattalin arziki da cinikayya, aikin soja, dokoki, al'adu da dai sauransu.

A nasa bangaren, Tillerson, ya bayyana cewa, bisa sauye-sauyen yanayin duniya, ana bukatar Amurka da Sin su kara yin hadin gwiwa da juna. Kasar Amurka tana son yin kokari tare da kasar Sin, da bin manufofin da shugaba Trump da shugaba Xi Jinping suka cimma daidaito, da tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak, da fadada hadin gwiwarsu bisa tunanin samun fahimtar juna, da girmama juna, da yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, ta haka za a inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

Hakazalika, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan halin da ake ciki a zirin Koriya da sauran batutuwan da suka lura tare. Wang Yi ya jaddada cewa, Sin ta ki amincewa da manufar Amurka na ajiye na'urar kakkabo makamai masu linzami wato THAAD a takaice a kasar Koriya ta Kudu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China