in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kori 'yan Somaliya kimanin 70 daga kasar
2017-03-11 13:05:07 cri
Ministan harkokin wajen Somaliya Abdirisak Omar Mohamed, ya tabbatar da cewa, kimanin 'yan kasar guda 70 da aka kora daga Amurka sun isa Mogadishu, babban birnin kasar a jiya Juma'a.

Abdirisak Mohamed wanda ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, a bana, wannan shi ne karo na biyu da Amurka ta kori 'yan kasar Somaliya daga kasarta, ya ce mutanen sun zauna a cibiyar tsare 'yan gudun hijira na kasar Amurka tsawon shekaru biyu, amma ba su samu iznin zama a kasar ba saboda sharudan doka.

Rahotanni sun bayyana cewa, ko a karshen watan Junairun bana, Amurkar ta kori 'yan kasar Somaliya 90 daga kasarta.

A ranar 21 ga watan Fabrairun da ya gabata ne, ma'aikatar tsaron kasa ta Amurka ta fidda wasu takardun doka guda biyu, inda ta kara adadin 'yan gudun hijira da za ta kora daga kasar, wadanda suka shiga kasar ba bisa doka ba.

Sanan ta kuma gaggauta ayyukan korar 'yan gudun hijira daga kasar, sakamakon matakan da ta dauka da suka hada da, kara adadin jami'an tabbatr da doka a hukumar kwastan da kuma hukumar kiyaye iyakar kasa da karawa ministan kiyaye tsaron kasa karfi, da kuma gina katanga a yankin kan iyaka dake tsakaninta da kasar Mexico. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China