in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin waje na Amurka zai kawo ziyara kasar Sin
2017-03-15 20:45:25 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying a yau Laraba ta bayyana cewa, sakataren harkokin waje na kasar Amurka Rex Tillerson, zai kawo ziyara nan kasar Sin daga ranar 18 zuwa 19 ga watan nan na Maris, bisa gayyatar takwaransa na kasar Sin Wang Yi.

A lokacin wannan ziyara, bangarorin biyu za su yi musayar ra'ayoyi a kan huldar da ke tsakanin kasashen biyu, da ma sauran harkokin duniya da na shiyya shiyya, wadanda ke daukar hankalinsu duka. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China