Bisa labarin da aka samu a jiya Litinin, an ce, shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya gana da shugaban al'ummar Falesdinu Mahmoud Abbas, a birnin Alkahira fadar mulkin kasar, inda shugabannin biyu suka jaddada muhimmancin daftarin "kasashe biyu", wanda aka kulla a tsakanin Isra'ila da Falesdinu, suna masu bayyana shi a matsayin mataki da zai ba da tabbaci, wajen cimma burin shimfida zaman lafiya da lumana a yankin Gabas ta tsakiya.
Bugu da kari, an ce, shugabannin biyu sun yi kira ga kasashen Larabawa, da su yi hadin gwiwa domin kare ikon al'ummomin Falesdinu bisa doka, da kuma ba da taimako wajen gina kasar Falesdinu mai 'yancin kai, bisa yankin iyaka da aka shata a shekarar 1967. (Maryam)