in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a kara azama kan ci gaba mai dorewa domin kara kawo wa dan Adam alheri
2017-03-21 12:59:35 cri

Jiya Litinin 20 ga watan nan, ranar farin ciki ce ta duniya. Albarkacin wannan rana, mataimakiyar babban magatakardar MDD Amina Mohammed, ta yi kira da a kara azama kan samun ci gaba mai dorewa, a kokarin kara sama al'ummar duniya da dinbin alherai.

Har wa yau a dai wannan rana, an gudanar da wani taro a babban zauren MDD, dangane da ranar farin ciki ta duniya, inda aka tattauna kan yadda gwamnatoci, da hukumomi, da mutane ke kara azama kan tsara manufar sada al'ummar duniya da alherai, a kokarin ganin bil Adama ya kara farin ciki a rayuwa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China