Kakakin gwamnatin kasar Congo-Kinshasa Lambert Mende ya bayyana cikin rahoton cewa, daya daga cikin ma'aikatan MDD guda biyu da aka yi garkuwa da su Ba-Amurke ne, kana dayan kuma dan kasar Sweden ne, baya ga wadannan ma'aikata biyu, an kuma yi garkuwa da wasu 'yan kasar Congo guda hudu wadanda suka tare da ma'aikatan a lokacin da wannan lamari ya auku.
Gwamnatin kasar Congo da tawagar musamman ta MDD dake aikin kiyaye zaman lafiya a kasar sun dukufa domin ceto wadanda aka yi gurkuwa da su, a sa'i daya kuma, hukumar shari'a tana bincike kan wannan lamari.
Rahotanni na cewa, dakarun dake adawa da gwamnati su kan tayar da hankula a lardin tsakiyar Kasai dake tsakiyar kasar Congo-Kinshasa, don haka, MDD ta tura wata tawagar masana zuwa wurin domin ta yi nazari, ta kuma gabatarwa kwamitin sulhu na MDD rahoto game da yanayin da kasar ke ciki a fannin tsaro. (Maryam)