A yau, a yayin wani taron manema labaru da aka shirya a nan Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, a kwanan baya, a karo na farko an sanya muhimmin tunanin "kafa wata kungiyar hada kai ta bil Adama" a cikin wani kudurin kwamitin sulhun MDD, wannan ya alamta cewa, hakan wani ra'ayi ne guda na kasa da kasa.
Bugu da kari, an zartas da kuduri mai lamba 2344 kan batun Afghanistan, a yayin taron kwamitin sulhun MDDr, inda aka yi kira ga kasa da kasa da su yi kokarin tallafawa kasar Afghanistan, tare da kara yin hadin gwiwar tattalin arziki a yankin, ta hanyar aiwatar da shirin "ziri daya hanya daya". (Sanusi Chen)