in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a ba da taimakon kudi dalar Amurka miliyan 166 ga Kenya
2017-03-17 11:58:31 cri
Wakilin MDD dake kasar Kenya Siddharth Chatterjee ya fidda wata sanarwa a jiya, inda ya yi kira da a samar da tallafin dallar Amurka miliyan 166 ga kasar Kenya, domin taimaka mata wajen fuskantar bala'in fari mai tsanani.

Sanarwar ta ce, adadin ruwan sama da aka yi a Kenya a shekarar 2016 bai kai na shekarun da suka gabata ba, lamarin da ya haddasa bala'in fari mai tsanani a garuruwa 23, musamman ma a wadanda dake arewacin kasar, al'amarin da ya haddasa karancin abinci, yaduwar cututuka da kuma mutuwar dabbobi da dama.

Haka zalika, bala'in farin ya haifar da matsaloli ga zaman rayuwar mutanen wuraren, har ma ya kai wasu ga barin gidajensu.

Bugu da kari, cikin sanarwar, Mr. Chatterjee ya yabawa gwamnatin kasar Kenya kan yadda take tunkarar matsalolin, inda ya kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su samar da taimakon kudi dalar Amurka miliyan 166 ga kasar, ta yadda za a tabbatar da samar da abinci da ruwan sha da kuma taimakon jinya ga al'ummarta sama da miliyan 2 cikin watanni 10 masu zuwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China