Haka zalika, an jaddada cewa, ya kamata a inganta hadin gwiwar sassa daban daban dake yankin domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankin, yayin da karfafa dunkulewar bil Adama.
Haka kuma, bayan an zartas da kudurin, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, a watan Janairun bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi jawabi a hedkwatar MDD dake birnin Geneva, inda ya bayyana muhimmiyar ma'anar karfafa dunkulewar bil Adama, da kuma fidda dabarar Sin kan yadda za'a nemi cigaban kasa da kasa da wayewar kan bil Adama.
A wannan karo kuma, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin mai lamba 2344, inda yake kunshe da manufar gina makomar bil Adama cikin hadin gwiwa, lamarin da ya nuna ra'ayi daya da gamayyar kasa da kasa suka cimma, da kuma babbar gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen kyautata yanayin duniya. (Maryam)