Yury Fedotov, babban daraktan UNODC, ya shedawa taron hukumar yaki da haramtattun kwayoyi karo na 60, ya fadi cewa matakan ci gaba ba yana nufin rage noman coca, da opium poppy da kuma ganyen cannabis ba ne, sai dai yana kokarin inganta yanayin koma bayan da rayuwar al'ummomin yankunan da ake noma wadannan ganyayen ke fuskanta.
Da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Xinhua, Fedotov ya ce, al'ummomin wasu yankunan suna ci gaba da noman haramtattun ganyaye ne a sakamakon matsanancin talauci da suke fama dashi.
UNODC yana kokarin hada kai da mambobin domin hukunta masu fataucin haramtattun kwayoyin, don tabbatar da adalci da kiyaye lafiya a wadannan bangarori, da kuma kara tallafawa matakan hukunta masu aikata kananan laifuka.
Fedotov ya ce, tawagarsa suna yin aiki tare da jami'an hukumar lafiya ta duniya (WHO) a fannnoni masu yawa, da suka hada da muhimman hanyoyin da za'a bi wajen dakile ayyukan masu ta'ammali da haramtattun kwayoyi domin zartas da hukuncin da ya dace a kansu. (Ahmad Fagam)