Wannan takardar mai shafuka 77 ta bayyana ka'idoji 12 na shirin gwamnatin Burtaniya game da ficewa daga EUn. A fannin cinikayya, kasar Burtaniya za ta fice daga kasuwar bai daya ta Turai, da kawancen harajin kwastam na EU, amma sassan biyu za su kulla wata sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, ciki har da cimma wata yarjejeniyar 'yancin cinikayya da harajin kwastam, da kokarin daddale sabuwar yarjejeniyar cinikayya tare da sauran kasashe. A fannin harkar kula da makaurata ma, kasar dinta Burtaniya za ta yi amfani da sabon tsari don kula da harkokin da suka shafi 'yan kasashen Turai, tare kuma da baiwa masana'antu isassun lokuta don dace da sabuwar ka'idar, baya ga haka a yayin da ake kare hakkin jama'ar kasashen Turai da tuni suke cikin Burtaniya, a sa'i daya kuma za a tabbatar da kare 'yancin 'yan kasar Burtaniya dake kasashen EU. A fannin shari'a, kasar Burtaniya za ta fice daga tsarin kotun Turai, amma za ta bullo da wani sabon tsari da nufin kawar da wasu matsaloli, ciki har da rikicin cinikayya da dai sauransu, kana za ta ci gaba da hada kai tare da EU don murkushe aikata laifuka da yaki da ta'addanci. (Bilkisu)