Ministan harkokin wajen Sin: Ya kamata a tallafawa al'ummomin Afirka yadda ya kamata
A jiya Juma'a, yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 a birnin Bonn na kasar Jamus, Ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya ce ya kamata a kiyaye wasu manufofi uku, idan har ana son samun sakamako mai kyau ta fuskar raya dangantakar dake tsakanin kasashen Afrika da sauran kasashen duniya.
Wang Yi ya ce, manufofin sun hada da, mai da hankali kan kiyaye zaman lafiya yayin neman samun ci gaba, da biyan bukatun kasashen Afirka, da kuma daukar matakan da za su dace wajen taimaka musu samun ci gaba; musamman a fannonin wanzar da zaman lafiya, inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma isashen abinci ga al'ummomin nahiyar da dai sauransu. (Maryam)