Inda ya bayyana ra'ayoyi da matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi yadda za a aiwatar da jadawalin samun dauwamammen ci gaba na da shekarar 2030, da dangantakar dake tsakanin sauran kasashen duniya da kasashen Afirka, da kuma yadda za a iya kiyaye zaman lafiya a hali mai sarkakiya da aka ciki a nan duniya da dai sauransu.
Wang Yi ya ce, kasar Sin tana sa ran gamayyar kasashe za su kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa, yayin da suke kokarin raya tattalin arziki bisa ka'idojin neman ci gaba, da kulla kawance da kuma bada dama ga sauran kasashe, da fahimtar juna, ta yadda za a hada kai wajen samun ci gaba, da kafa sabuwar dangantakar tsakanin kasa da kasa.
Sa'annan, ya yi kira da sanya jadawalin neman dauwamammen ci gaba nan zuwa shekarar 2030, cikin shirin tabbatar da ci gaban kasashen duniya.
A ganin kasar ta Sin, ya kamata a mai da hankali kan kiyaye zaman lafiyar duniya, yayin neman ci gaba da hadin gwiwa, sannan kuma, a girmama ra'ayoyin kasashen Afirka, tare da ba su taimako yadda ya kamata a lokacin da suke dukufa wajen samun ci gaba.
A halin yanzu, kasar Sin tana aiwatar da manufofinta bisa tsare gaskiya da nuna adalci, yayin ba da taimako ta hanyoyin da suka dace ga kasashen Afirka.
Bugu da kari, Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka, wajen neman bunkasa cikin zaman lafiya, inda ta dukufa kan ayyukan kiyaye zaman lafiyar duniya.
Haka kuma, tana son karfafa hadin gwiwarta da gamayyar kasashe, kan aikin kiyaye zaman lafiya da na tsaron kasa da kasa. (Maryam)