in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Ya kamata a inganta hadin-gwiwa domin tunkarar kalubale
2017-02-17 11:21:11 cri
A jiya Alhamis ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron farko na ministocin harkokin wajen kasashe maso karfin tattalin arziki wato G20 a birnin Bonn na kasar Jamus, inda ya jaddada cewa, samun ci gaba mai dorewa nauyi ne dake kan dukkanin kasashe. Saboda haka, ya yi kira ga kasashen duniya da su zama tsintsiya madaurinki daya, a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya, da raya sabuwar dangantakar dake tsakanin kasashe daban-daban dake kawowa juna moriya.

Dadin dadawa, Mista Wang Yi ya ce, ya zama dole kasashe daban-daban su himmatu wajen raya tattalin arziki ta hanyar da ta dace, da neman ci gaba mai dorewa a fadin duniya. Haka kuma, a yi kokarin rage gibin dake tsakanin mawadata da matalauta, da kuma karfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashe maso tasowa da kasashe masu sukuni, ta yadda za'a kulla wata sabuwar dangantaka tsakanin kasashen duniya, wadanda za su samu bunkasuwa kafada da kafada da juna.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China