Kungiyar hada kan kasashen Larabawa ta yi Allah wadai da dokar da Isra'ila ta bullo da ita wadda ta ba ta iznin gina rukunin matsugunan yahudawa a yankunan Palasdinawa da ke yammacin kogin Jordan.
Jagoran kungiyar AL da ke Alkahira na kasar Masar Ahmed Aboul Geit wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce, Isra'ila ta fake da wannan doka ce kawai don ta kwace filayen palasdinawa.
A karkashin sabuwar dokar, za a gina sabbin gidaje kimanin 3,850 a yankuna daban-daban na al'ummar Palasdinawa da aka kwace ba bisa ka'ida ba.
Ahmed Gheit ya bayyana cewa, dokar tana daya daga cikin manufofin da Isra'ila ta bullo da ita da nufin kawar duk wani yunkuri na kafa kasashe biyu da kuma yunkurin kafa kasar Palasdinawa mai cin gashin kanta.
Sanarwar ta ce wannan doka ta bayyana aniyar gwamnatin Isra'ila a fili da kuma yunkurinta na watsi da duk wani mataki na wanzar da zaman lafiya.
A jiya ne majalisar dokokin Isra'ila ta amince da wannan doka bisa yawan kuri'un amince 60 da kuma kuri'u 52 da ba sa goyon bayan dokar.(Ibrahim)