Sai kuma wata sanarwa da fadar shugaban Palesdinu ta fitar, ta yi Allah wadai da matakin Isra'ila na ba da iznin gina matsugunan Yahudawa a gabashin birnin Kudus, inda ta kalubalanci kasashen duniya da su matsawa Isra'ila lamba ta martaba kudurin MDD kana ta gaggauta yin watsi da shirinta na gina matsugunan. (Zainab)