Kwamitin sulhu na MDD, ya gaza amincewa da kudurin dake da nufin kakabawa Syria takunkumi, saboda zarginta da ake da amfani da makami mai guba, inda Rasha da China suka kada kuri'ar naki yayin zaman kwamitin na jiya.
Mambobin kwamitin tara ne suka kada kuri'ar amincewa da kudurin da Birtaniya da Faransa da Amurka suka gabatar, sabanin Rasha da Sin da Bolivia da suka kada kuri'ar kin amincewa yayin da Kazakhstan da Eqypt da Habasha suka ki kada kuri'a'.
Jakadan kasar Sin a MDD, Liu Jieyi ya shaidawa kwamitin bayan kada kuri'ar cewa, har yanzu ana gudanar da bincike kan batun, don haka ya yi wuri ace za a yanke hukunci.
Ya yi kira ga kwamitin ya mara baya ga binciken hadin gwiwa ta hanyar nuna kwarewa, tare da daukar matakin da ya dace bayan an samu sahihan bayanai da shaidu.
Ya ce ba su amince wata kasa ko hukuma ko daidaikun mutane su yi amfani da makami mai guba ba a kowane irin yanayi.(Fa'iza Mustapha)