in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Siriya sun karbe ikon garin Palmyra
2017-03-03 13:32:01 cri
Sojojin gwamnatin kasar Siriya sun bayyana jiya Alhamis cewa, sun yi nasarar karbe ikon tsohon garin Palmyra dake yankin tsakiyar kasar.

A cikin wata sanarwar da rundunar sojan kasar Siriya ta fitar, an ce, sakamakon goyon-bayan da sojojin saman Rasha da Siriya suka bayar, sojojin Siriya sun fatattaki dakarun kungiyar nan ta IS, lamarin da ya sa suka karbe garin Palmyra gami da kewayensa. A halin yanzu, ana kokarin kawar da abubuwan fashewa da dakarun IS suka dana.

Sanarwar ta ce, sojojin gwamnatin Siriya sun samu ci gaba wajen yakar dakarun kungiyar IS a jihar Aleppo dake arewacin kasar, abun da ya kasance babbar galaba da sojojin gwamnatin kasar suka samu kan dakarun na IS.

Har wa yau kuma, sanarwar ta jaddada cewa, sojojin gwamnatin Siriya gami da sojojin kawancensu, su kadai ne ke iya murkushe ayyukan ta'addanci, za kuma su ci gaba da yaki da kungiyar IS da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China