in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 16 sun mutu sakamakon faduwar wata katuwar bishiya a magangarar ruwa a Ghana
2017-03-20 12:05:14 cri

 

Wata katuwar bishiya ta fada a dab da wata magangarar ruwa a yankin Kintampo a lardin Brong-Ahafo da ke kasar Ghana a ranar 19 ga wata, inda masu yawon shakatawa a kalla 16 suka rasa rayukansu, wadanda yawancinsu 'yan makarantar sakandare ne da ke bude ido a magangarar ruwan, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Bayan abkuwar hadarin, masu ba da agaji na wurin sun iso wurin da hadarin ya abku, sun kuma kai wadanda suka ji rauni a asibiti. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China