Da yake jawabi ga wakilai daga Bankin hada kai na Afirka wato UBA, shugaban kasar, ya ce gwamnatinsa ta kama aiki ne saboda tattalin arzikin kasar ya samu koma baya, kuma akwai bukatar daukar sabon mataki.
Ya ce aikin farko da gwamnatinsa za ta yi shi ne, farfado da tattalin arziki tare da sanya shi a tafarkin ci gaba da bunkasa, yana mai cewa, gwamnatin na son habaka bangaren sana'o'i da aikin gona, tare da samar da ingantaccen tsarin samar da kudi da zai tallafawa bangarorin biyu. (Fa'iza Mustpha)