Mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumai, ya bukaci kasashen Afrika su karfafa hadin kai da nufin samun habakar tattalin arzikin yankin cikin sauri.
Mahamudu Bawumai wanda ya yi kiran a jiya Talata, yayin bude wani taron yini biyu na 'yan asalin nahiyar dake zaune a kasashen ketare, ya jadadda bukatar habakar nahiyar ta yadda za ta tsallake matakin samun tallafi daga kasashen duniya zuwa na dogaro da kanta.
Ya ce yadda ake kallon nahiyar a gida da waje ya dogara ne a kan tattalin arzikinta, yana mai cewa, kamata ya yi a hada karfi da karfe don ganin nahiyar ta samu ci gaba ta fuskar tattalin arziki, ta yadda za ta iya tsayawa da kafarta.
Har ila yau, mataimakin shugaban kasar Ghanan ya bukaci kasashen nahiyar su yi koyi da kasar Sin da sauran kasashen nahiyar Asiya, wadanda bisa jajircewa da kwazo, suka kai matakin da suke a yanzu. (Fa'iza Mustapha)