in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta baiwa asibitin LEKWA gudumawar kayayyakin aiki
2017-03-14 09:23:55 cri
Gwamnatin kasar Sin ta baiwa asibitin Ledzokuku-Krowor dake kasar Ghana (LEKMA) gudummawar kayayyakin aiki da darajarsa ta kai sama da dalar Amurka 150,000.

Manufar wannan gudummawa ita ce kara yawan kayayyakin aikin da asibitin ke amfani da su a bangaren harkokin kiwon lafiya.

A jawabinsa yayin bikin mika kayayyakin, kansila mai kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya a ofishin jakadan kasar Sin da ke Ghana Chai Zhijing, ya bayyana cewa, kasashen biyu na amfana matuka da dangantakar da ke tsakaninsu.

Ya ce, ya yi farin ciki sosai da samun labarai cewa, asibitin wanda gwamnatin kasar ta gina a shekarar 2010, ya kula da marasa lafiya kimanin 100,000 a shekarar 2016 da ta gabata. Kuma kayayyakin za su kara samar da kiwon lafiya mai inganci ga 'yan kasar ta Ghana.

Kayayyakin sun hada da gadajen haihuwa, da kujerun tura marasa lafiya da na'urorin aikin fida da kayayyakin aikin fida na bangaren mata da na'urorin gwada nauyin jarirai na zamani da sauransu.

Shi ma a nasa jawabin darektan mai kula da magungunan gargajiya da na zamani a ma'aikatar lafiyar kasar Ghana, Anastasia Yirenkyi ya yaba da taimakon da gwamnatin kasar Sin ta dade tana baiwa gwamnatin Ghana a bangaren kiwon lafiya.

Baya ga asibitin na LEKMA, gwamnatin Sin ta kuma tallafawa asibitin koyarwa na Korle-Bu, da kuma wasu marasa lafiya sama da 200 da ke fama da ciwon zuciya wadanda ke jinya a asibitin koyarwa na Komfo Anokye dake birnin Kumasi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China