in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana tana saran samun kaso 6.3 na GDP a shekarar 2017
2017-03-03 10:21:16 cri
Gwamnatin kasar Ghana ta bayyana cewa, a cikin shekarar 2017 da muke ciki, tana fatan samun bunkasuwar kaso 6.3 cikin 100 na GDP da kaso 4.6 cikin 100 a bangaren GDPn da bai shafi mai ba.

Ministan kudi na kasar Kenneth Ofori-Atta wanda ya shaidawa majalisar dokokin kasar hakan a jiya Alhamis, ya kuma ba da tabbacin cewa, gwamnati ta kara inganta hanyoyin samun kudaden shigarta a wani mataki na cike gibin kaso 6.5 cikin 100 na GDPn kasar kafin karshen shekara.

Wadannan matakai a cewarsa, sun hada da toshe duk wasu hanyoyi da kudaden shigar gwamnati ke sulalewa da rage wasu haraji da ake karba, baya ga kara bullo da wasu hanyoyi da kasar ke samun kudaden shigarta.

Ministan ya ce, daga yanzu, gwamnati za ta karkata daga tsarin ta na raya tattalin arziki ta hanyar karbar haraji zuwa samar da kayayyaki. A hannu guda kuma gwamnati za ta sake nazarin wasu harajin da ta ke karba, yayin da za ta soke wasu harajin baki idan har akwai bukatar yin hakan.

Haka kuma, gwamnati za ta kara fadada ragowar sassan tattalin arzikinta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China