in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar Ghana ta karbi bakuncin taron daukar ma'aikata a kamfanonin Sin dake kasar
2017-03-19 12:26:44 cri

A jiya Asabar cibiyar nazarin al'adun Sinawa ta Confucius dake Jami'ar Ghana tare da hadin gwiwar masana'antun kasar Sin dake Ghana ta gudanar da taron neman daukar ma'aikata ga dalibai da wadanda suka kammala karatu, na guraben aiki 230 a kamfanonin kasar Sin 35 dake kasar Ghana.

Mei meilian, ita ce daraktar cibiyar ta Confucius a Jami'ar ta Ghana, ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, sama da mutane 1,000 ne suka gabatar da bukatar neman aikin.

Mei ta ce, wannan shi ne karon farko da cibiyar Confucius ta hada kamfanonin Sin da daliban jami'ar har ma da sauran jama'ar gari.

Chai Zhijing, jami'in kasuwanci da tattalin arziki a ofishin jakadancin Sin dake kasar Ghana, ya yabawa cibiyar ta Confucius da hukumomin gudanarwa jami'ar saboda bullo da wannan shiri, kana ya bukaci a kara bunkasa irin wadannan muhimman shirye-shirye.

Mataimakin shugaban jami'ar ta Ghana Farfesa Samuel Kwame Offei, ya ce wannan shirin zai taimakawa kokarin da jami'ar ke yi na kara kusantar da dalibai ga masana'antu domin samun damammaki.(Ahamd Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China