Da yake karin haske game da muhimmancin wannan aiki a jiya Lahadi, shugaba Akufo-Addo, ya ce ginin zai killace muhimman bayanai, da makaloli, da tufafi, da litattafai, wadanda shugabannin kasar na baya suka yi amfani da su, domin hakan ya zamo alama ta gudummawar da suka baiwa kasar, yayin da suke jagorancin ta.
Shugaban ya kuma yi amfani da bikin kaddamar da ginin, wajen bude wani baje koli na musamman, wanda zai nuna irin yadda 'yan mazan jiya suka sadaukar da rayukan su, domin cimma nasarar samun 'yancin kai da ciyar da kasar ta Ghana gaba.
Akufo-Addo ya kuma yi fatan wannan baje koli zai karkata tunanin 'yan kasar sa, ga muhimmancin amfani da kuzari da basirar su wajen bunkasa kasar, kamar yadda hakan ke kunshe cikin taken cikar kasar shekaru 60 da kafuwa, wato "Zaburarwa domin samun nasara a nan gaba". (Saminu Alhassan)