Yau Litinin ne aka labarta cewa, kasar Koriya ta Arewa ta harba wani abun da ba a san ko mene ne ba a tekun da ke gabashin zirin Koriya.
Dangane da labarin, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a nan Beijing cewa, tuni kwamitin sulhu na MDD ya takaita yadda Koriya ta Arewa za ta iya amfani da fasahar makamai masu linzami wajen gudanar da gwaje-gwajenta. Kasar Sin ba ta goyon bayan Koriya ta Arewa ta sabawa kudurin kwamitin sulhu, ko kuma ta harba wani abu mai kama da makami mai linzami. (Tasallah Yuan)