in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na son karbar shawarwari daga bangarori daban daban kan yadda za a warware matsalar zirin Koriya
2017-03-11 13:10:19 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasarsa na son tattaunawa tare da karbar shawarwari daga bangarori daban-daban, kan yadda za a warware matsalar zirin Koriya.

Geng Shuang da ya bayyana haka a jiya Juma'a yayin wani taron maneman labarai, ya ce babban kalubalen shi ne, bangarorin da matsalar zirin Koriya ta shafa, ba su amince da juna ba, yana mai cewa kamata ya yi a nemi wata dabarar da za ta dace da bukatun sassa daban-daban, domin warware matsalar daga tushe.

Ya ce kasar Sin na fatan ganin bangarori da abin ya shafa, sun tattauna tare da yin nazari yadda ya kamata, kan shawarwarin da kasar Sin za ta samar musu, yayin warware matsalar bisa ka'idojin kiyaye zaman lafiya da kuma kawar da makamashin nukiliya a yankin.

Baya ga karbar shawarwari daga bangarorin daban-daban kan yadda za a warware matsalar, Geng Shuang ya ce kasar Sin, za ta ci gaba da tattaunawa da bangarorin da abin ya shafa ta yadda zai kai su ga hawa teburin neman sulhu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China