in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kalubalanci Amurka da Koriya ta Kudu su dakatar da shirinsu na girke na'urorin kakkabo makama masu linzami na THAAD
2016-07-08 16:16:27 cri
A yau safe ne ma'aikatar tsaron kasar Koriya ta Kudu ta sanar da cewa, kasarta da kasar Amurka sun amince su girke na'urorin kakkabo  makamai masu linzami sanfurin THAAD a kasar Koriya ta Kudu. Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayar da sanarwar nuna rashin amincewa game da wannan batu. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana a nan birnin Beijing cewa, girke wadannan na'urori ba zai taimaka wajen cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya da kuma kiyaye zaman lafiya a zirin ba, sai ma ya kara kawo illa ga moriyar kasashen dake yankin ciki har da kasar Sin. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China