in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ce kadai ta amfana daga halin da ake ciki a zirin Koriya
2016-08-04 11:32:51 cri
Mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin kasa da kasa na majalisar dattijai ta kasar Rasha Igor Klimov ya bayyana a jiya Laraba cewa, kasar Amurka ce ta harzuka kasar Koriya ta Arewa har ta ke fadada shirin ta na kera makamai, daga bisani kuma, ta ke ikirarin neman jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami a kasar Koriya ta Kudu don tinkarar barazanar Koriya ta Arewa. Yanzu dai kasar Amurka ce ita kadai ta amfana da kiyayyar da ta kunno kai a zirin Koriya da yankin gabashin Asiya.

Klimov ya bayyanawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Russian Today a wannan rana cewa, kasar Amurka ta kara yawan sojoji da makaman da ta ke jibgewa a kasashen Japan da Koriya ta Kudu, matakin da ya ke matsawa kasar Koriya ta Arewa lamba ta mayar da martani ta hanyar gwajin makamanta masu linzami.

Bisa la'akari da zangon da makamai masu linzami za su iya kaiwa, gwajin makaman da Koriya ta Arewa ta yi zai fi yiwa kasar Rasha barazana idan aka kwatanta da kasar Japan.

Klimov ya yi imanin cewa, akwai bukatar kasar Koriya ta Arewa ta martaba kudurin kwamitin sulhun MDD, da kuma yin shawarwari tare da bangarorin da abin ya shafa. Haka kuma kamata ya yi kasashen Japan da Koriya ta Kudu su fahimci cewa, yin amfani da hanyar kara hadin gwiwar tattalin arziki a zirin Koriya zai taimakawa Koriya ta Arewa da ta Kudu shiga a dama da su cikin manyan ayyukan tattalin arziki, ta yadda za a kawar da duk wata barazana a yankin. Idan ba haka ba, ba za a samu kyautatuwar yanayi a yankin ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China