in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun kalubalanci Koriya ta Arewa da ta dakatar da harba makamai masu linzami
2017-03-07 10:50:12 cri
Kasashen duniya sun ja hankalin Koriya ta Arewa, da ta dakatar da gwajin makamai masu linzami da take harbawa.

Mataimakin kakakin babban sakataren MDDr Farhan Haq, ya rawaito babban sakataren majalissar António Guterres, na la'antar matakin Koriya ta Arewan na harba makamai masu linzami. Mr. Guterres ya ce hakan ya sabawa kudurin kwamitin sulhu, kana ya kalubalanci Koriya ta Arewa da ta dakatar da aikata hakan.

Ya ce yana gargadin kasar da kada ta sake karya dokar kwamitin sulhun, ta kuma sauke nauyin dake wuyan ta na kare dokokin kasa da kasa. A cewarsa, yanzu haka kwamitin sulhun na tantance yanayin da ake ciki a yankin.

A na ta bangare, fadar gwamnatin Amurka ta White House a jiya Litinin, ta bayyana cewa, aikin harba makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ta yi barazana ce ga sauran kasashe dake zirin Koriya. Kakakin White House Sean Spicer ya bayyana cewa, kasarsa za ta hada kai tare da kawacenta, don tinkarar kalubalen da Koriya ta Arewa ke kawowa.

Da sanyin safiyar jiya Litinin ne dai rundunar sojan kasar Koriya ta Kudu, ta ce Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami har guda 4 daga Pyonganpuk-do zuwa tekun gabashin zirin Koriya. Wannan ne kuma gwajin harba makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ta yi a karo na 2 a baya bayan nan cikin wata guda.

Kamfanin dillancin labaru na Koriya ta Arewa ya bayar da labari a yau Talata cewa, shugaban kasar Kim Jong Un ne da kan sa, ya jagoranci rundunar sojan kasar wajen kaddamar da gwajin makaman masu linzami. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China