Kotun ta sanar da hakan ne a yau Talata, bayan da alkalan kotun kolin suka yanke hukuncin da ya goyi bayan wasu kungiyoyin jama'a da suka kalubalanci matakin gwamnatin Burtaniya wajen amfani da doka ta 50 game da shirin fara tattaunawar ficewarta daga kungiyar tarayyar Turai.
Yanzu matakin kotun kolin kasar ya baiwa 'yan majalisar dokoki damar kada kuri'a kafin fara aiwatar da shirin. Sai dai wannan mataki na kotun kolin bai yi wa gwamnatin dadi ba. (Ibrahim)