in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da Kenya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta bangaren yawon bude ido a kasar
2017-02-16 09:56:37 cri

Hukumar samar da matsuguni ta MDD da kasar Kenya, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta bangaren yawon bude ido, ta hanyar kyautata tsarin muhalli.

Shugaban sashen samar da lantarki a birane na hukumar ta MDD da ake kira da UN Habitat Dr. Vincent Kitio, ya shaidawa manema labarai a Nairobi cewa, karkashin yarjejeniyar, UN Habitat za ta rika bada shawarwarin da suka kamata ga hukumar dake samar da kudade ga bangaren yawon bude ido ta kasar Kenya TFC, kan yadda za a rika tsara otel-otel, da kuma yi wa wadanda ake da su kwaskwarima, ta yadda za su dace da fasahar zamani.

Kitio ya ce manufar ita ce, samar da ingantaccen lantarki a tsarin otel-otel, ta yadda za a tabbatar da kyakkyawan yanayin muhalli mai dorewa.

Baya ga haka, wani muhimmin batu cikin yarjejeniyar shi ne, taimakawa ma'aikatan fasaha na hukumar TFC da kayayyakin aiki da kuma matakan da za su taimaka musu wajen tsara gine-ginen da ba za su rika jan wuta da ruwa ba.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China