Majiyoyi daga rundunar 'yan sandan sun bayyana cewa, an dawo da mutanen da suka hada da namiji mai shekaru 20 da mace 'yar shekara 26 daga Turkiyya, inda suka sulale suka shiga kasar bayan sun karbi horo a Syria.
Kwamandan 'yan sandan Mombasa Peter Maelo, ya ce yanzu haka, ana yi wa mutanen tambayoyi don samun Karin haske game da ayyukan kunyar a Kenya.
Ya ce tun a watan Nuwamban da ya gabata aka fara bibiyar mutanen cikin sirri, bayan hukumomin Turkiyya sun shaidawa kasar Kenya alakarsu da kungiyar IS.
Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, jami'an tsaro sun tsananta aikinsu a cikin Mombasa da sauran garuruwan dake gabar ruwa, da nufin dakile duk wani yunkuri na kai harin ta'addanci.( Faiza Mustapha)