in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Kenya ta yabawa yunkurin kasar Sin wajen kare gandun dabbobi
2017-02-08 10:02:10 cri

Wata jami'ar gwamnatin Kenya ta yabawa kokarin kasar Sin wajen kare gandun dabbobi yana mai cewa, matakin da kasar Sin ta dauka na haramta cinikin hauren giwa zai taimaka wajen kare giwaye a kasar ta gabashin Afrika.

Judi Wakhungu, ita ce sakatariyar ma'aikatar kare muhalli da albarkatun kasa ta Kenya, ta shedawa kamfanin dillancin labaran Xinhua a lokacin bikin cika shekaru 60 da kungiyar kare gandun dabbobi ta gabashin Afrika wato EAWLS a takaice, ta bayyana cewa hadin giwar dake tsakanin kungiyar da kasar Sin tana kara tabbatar da bada kariya ga lafiyar dabbobi da kuma kara inganta fannin kula da gandun dabbobi, musamman bisa irin gudunmawar da kasar Sin ke baiwa wannan fanni wajen bada samar da kayayyakin kula da dabbobin da kuma yadda take taka rawa wajen bada kariya ga lafiyar dabbobin.

Da take karyata zargin da ake cewa aikin gina layin dogo daga Mombasa zuwa Nairobi yana kawo illa ga lafiyar dabbobi, Wakhungu ta ce, wannan aiki ya tanadi shiri na musamman na baiwa dabbobi kariya daga fuskantar duk wata matsala.

Ta ce alal misali, aikin layin dogo na Mombasa-Nairobi an samar da SGR musamman domin dabbobin su samu hanyoyin wucewa da kwalbatoci da gadoji wanda aka tanada domin dabbobin. Haka zalika, SGR ya tanadi shinge domin gujewa duk wani abu da zai haifar da illa ga rayuwar dabbobin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China