Ministan kudin Kenya Henry Rotich, da jakadan kasar Sin dake Kenyar Liu Xianfa, da mataimakin babban manajan kamfanin PowerChina Wang Bin ne suka halarci bikin bude kamfanin.
Mista Henry Rotich ya bayyana cewa, kasar Sin muhimmiyar aminiya ce ta Kenya, kuma hadin-gwiwar kasashen biyu ta fuskar tattalin arziki na kara ingantuwa. Mista Henry ya ce, kafa babbar hedikwata a Kenya da kamfanin PowerChina ya yi, na nuni da irin karfin dangantaka dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangaren, jakada Liu Xianfa ya ce, kamfanin PowerChina ya bayar da babbar gudummawa a fannin raya Afirka gami da kyautata zamantakeware mutanen nahiyar.
Liu ya kuma yi fatan kamfanin PowerChina zai ci gaba da kokarinsa na kyautata harkokin da yake gudanarwa a Afirka, da kara karfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa, PowerChina, wani hamshakin kamfanin kasar Sin ne dake gudanar da ayyukan da suka shafi makamashi, wutar lantarki, ayyukan more rayuwar al'umma, ruwa, muhalli da sauransu. Tuni dai wannan kamfani ya kafa hedikwatarsa a yankin Asiya da Pasific, da kuma yankin tsakiya da yammacin nahiyar Afirka.
Wannan sabuwar hedikwatar da kamfanin ya kafa a kasar Kenya, zai kula da ayyukan da suka shafi kasashe 26, ciki har da Kenya, Habasha, Uganda, Tanzaniya, Zambiya, Zimbabwe, Afirka ta Kudu da sauransu.(Murtala Zhang)