Jami'in 'yan sandan yankin Joseph Chebusi ya shaidawa manema labarai cewa, jami'ansa sun yi nasarar kwato gurneti da wasu mugun makamai a wajen maharan da suka dawo daga kasar Somaliya
Ya ce tun ba yau ba ,'yan sanda sun dade suna neman daya daga cikin maharan da aka kashe mai suna Juma Mwamuraji mai shekaru 44 tun bayan da ya dawo daga kasar Somaliya.
Chebusi ya ce 'yan sanda sun harbe Juma ne lokacin da ya yi kokarin jefansu da gurnetin da ke hannunsa. Bayanai na nuna cewa, a shekarar 2016 yankin kwale ne ke kan gaba wajen yawan mayakan Al-Shabaab da suka dawo kasar ta Somaliya, sai yankunan Kilifi da Mombasa da kuma Lamu.
Sai dai kuma 'yan sanda na gargadin jama'a da su yi hattara game da barazanar mayakan na Al-shabaab, tun bayan da suka bazu a cikin dazuka, inda suke amfani da wuraren a matsayin sansanin daukar magoya baya tare da shirya yadda za su kaddamar da hare-hare a yankin.
Yanzu haka dai gwamnatin kasar Kenya ta fitar da jerin sunaye da hotunan mutane bakwai 'yan kungiyar Jaysh Aman da take nema ruwa a jallo, har ma ta sanya ladar dala dubu 20 ga duk wanda ya taimaka mata da bayanai da za su kai ga damke su. (Ibrahim Yaya)