in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron shawarwarin Sin da Burtaniya karo na 8 a birnin London
2016-12-21 09:57:20 cri
A jiya Talata ne aka bude taron shawarwari tsakanin kasar Sin da kasar Burtaniya bisa manyan tsare-tsare karo na 8 a birnin London na kasar Burtaniya, inda mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi da sakataren harkokin wajen kasar Burtaniya Boris Johnson suka jagoranci taron.

A yayin taron, Yang Jiechi ya bayyana cewa, a yayin ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Burtaniya a shekarar da ta wuce, shugabannin kasashen biyu sun cimma ra'ayi daya dangane da gina dangantakar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Burtaniya bisa manyan tsare-tsare a karni na 21, haka kuma, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Burtaniya don ganin an aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma, ta yadda za a karfafa shawarwari a tsakanin kasashen biyu, da zurfafa fahimtar juna da hadin gwiwa a fannin siyasa, ta yadda za a ciyar da bunkasuwar dangantakar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Burtaniya gaba, da ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.

A nasa bangare, Boris Johnson ya bayyana cewa, kasar Burtaniya tana tsayawa tsayin daka wajen raya dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kasar Sin bisa manyan tsare-tsare, kuma za a shiga "muhimmin lokaci" na raya dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. Kasar Burtaniya tana son karfafa mu'amalar dake tsakaninta da kasar Sin bisa manyan tsare-tsare, domin inganta hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki, zuba jari da ababen more rayuwa da dai sauransu, ta yadda za a fuskanci manyan kalubalolin da duniya ta ke fama da su cikin hadin gwiwa, yayin da karfafa fahimtar juna kan wasu batutuwan kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China