Sanarwar ta bayyana cewa, wadannan hukumomin kasa da kasa hudu sun yi kira ga kungiyoyin siyasa daban daban na kasar Congo Kinshasa da su yi hakuri da juna, da kalubalantar magoya bayansu da su magance tada rikice-rikice. Hukumomin sun bayyana cewa, za su ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Congo Kinshasa da ta yi shawarwari a tsakanin 'yan kasar, tare da jaddada cewa, ba a iya aza tubali ga aiwatar da zaben shugaban kasar yadda ya kamata sai idan an cimma daidaito da juna ta hanyar yin shawarwari a tsakanin bangarori daban daban na kasar.
Bisa shirin da aka tsara, za a gudanar da zaben shugaban kasar Congo Kinshasa a ranar 20 ga wannan wata, amma hukumar zaben kasar ta bayyana cewa, kamata ya yi a sabunta rijistan zabe, don haka aka jikirtar da gudanar da zaben. Amma jam'iyyun adawa sun yi watsi da wannan kuduri. Tun daga ranar 19 ga wannan wata, jam'iyyun adawa na kasar sun yi zanga-zanga a birnin Kinshasa, inda masu zanga-zanga fiye da dubu daya suka yi fito na fito tare da jami'an tsaro, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 32. (Zainab)