A cikin wata sanarwa, kwamitin ya jaddada wajabcin gaggautar dake da akwai wajen kira tattaunawar siyasa da za ta kunshi dukkan bangarorin dake ruwa da tsaki, musammun ma kan maida hankali ga shirya zabuka.
Kwamitin sulhu ya kuma bayyana damuwarsa kan karuwar haramce haramce a dandalin siyasa a kasar RDC-Congo, musammun ma kan kame kamen baya bayan nan na mambobin jam'iyyun sisaya dana kungiyoyin fararen hula. Haka kuma kwamitin ya bayyan babbar damuwarsa kan tauye hakkin jama'a da kuma jinkirin da ake samu wajen shirya zabuka. Kwamitin sulhu ya yi kira ga gwamnatin RDC, da kuma bangarorin da abin ya shafa, da su girmama 'yancin dan Adam da kuma kaucewa tashe tashen hankila da kuma tsokana. (Maman Ada)