in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RDC: MONUSCO na nuna damuwa sosai kan karuwar tashe-tashen hankalin siyasa
2016-10-12 10:03:23 cri

Wakilin musamman na sakatare janar na MDD, kana shugaban tawagar MDD dake kasar RDC-Congo (MONUSCO), Maman Sambo Sidikou, ya yi kashedi a ranar Talata kan kazancewar tashe-tashen hankalin siyasa, a yayin da kuma rikicin zaben ya zama wani rikicin kundin tsarin mulki.

Matsalar siyasa na tangal tangal sosai a RDC-Congo, lamarin dake kara rura wutar rikici matuka, da ci gaba da rage fagen siyasa da haifar da wani babban hadarin ganin matsalar ta kara tsananta, in ji mista Sidikou.

Jami'in ya bukaci kwamitin tsaro na MDD da ya yi amfani da karfinsa domin ba da kwarin gwiwa ga masu ruwa da tsaki na RDC-Congo da suka kauracewa shirin tattaunawa da su sake halarta da kuma bai wa gwamnati tabbacin gudanar da harkokin siyasa cikin 'yanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China