in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi maraba da yarjejeniyar zaman lafiya a DRC
2017-01-05 10:13:28 cri
A jiya Laraba kwamitin tsaron MDD yayi maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar warware rikicin siyasar jamhuriyar Dekokaradiyyar Congo tsakanin gwamnati da kungiyoyin yan tawayen kasar ta (DRC), wanda ake saran zai tabbatar da samun zaman lafiya wajen sauya shugabanci a kasar wacce ke tsakiyar Afrika.

A ranar Asabar ne aka rattaba hannu kan yarjejeniyar a Kinshasa tsakanin kungiyoyin 'yan adawa da kuma jagoran mulkin kasar Joseph Kabila. Yarjejeniyar ta bukaci shugaba Kabila ya sauka daga karagar mulkin kasar bayan kammala zabe, kuma dole ne a gudanar da zaben kafin karshen shekarar nan ta 2017.

Cikin sanarwar da kwamitin mai wakilcin kasashen 15 ya fitar ya ce, yana fata za'a aiwatar da yarjejeniyar domin a samu nasarar shirya zaben shugaban kasar cikin kwanciyar hankali, kuma a kammala kafa sabuwar gwamnati kafin watan Disambar 2017.

Kwamitin ya bukaci gwamnatin DRC da masu ruwa da tsaki a kasar, dasu dauki kwararan matakai wajen shirya babban zaben kasar ba tare da bata lokaci ba, kuma cikin wa'adin da aka amince dashi.

Sanarwar ta bukaci kawayen DRC da sauran kungiyoyin hulda na kasa da kasa dasu taimakawa kasar wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da tsaro.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China