A wajen taron manema labarai na zama na biyar na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 12, dan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kana fitaccen masanin tattalin arziki a kasar, Mista Li Yining ya ce, akwai yiwuwar saurin habakar tattalin arzikin kasar zai zarce kashi 6.5 bisa dari a shekarar da muke ciki, haka kuma Sin za ta kara cimma nasarori ta fuskar tattalin arziki.
Mista Li ya ce, kasar Sin na fuskantar manyan sauye-sauye, kuma ya zama dole kasar ta canja salonta na neman bunkasuwa, wato daga tsarin samar da ci gaba mai sauri zuwa tsarin samar da ci gaba mai inganci.
Li ya kuma kara da cewa, kamata ya yi kasar Sin ta yi sauye-sauye gami da kwaskwarima ga tsarinta na neman ci gaban tattalin arziki, lamarin da zai sa kasar ta samu sabon ci gaba.(Murtala Zhang)